Babu maganar karin farashin fetur a Nigeria—IPMAN

0
64
Man fetur a Najeriya

Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta kasa IPAN, ta ce babu wani shirin da take yi na kara farashin litar man fetur.

Kungiyar ta sanar da hakan ne ta bakin shugabanta na shiyyar arewa maso yamma, Bashir Salisu, lokacin da yake zantawa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka, wanda yace aikin da matatun fetur na kasar nan, keyi zai kara inganta fannin mai da kuma samar dashi a farashi mai sauki.

:::https://dailynews24ng.com/hausa/2025/01/16/babbar-mota-ta-kashe-mutane-9-a-cikin-gidan-su/

Shugaban yace zuwa yanzu babu daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar IPMAN, daya kara farashin mai.

Sai dai ya tabbatar da tashin farashin man dizel, inda ya kare matakin tashin farashin da cewa suma sun samu kari akan yadda suke saro shi, amma idan yayi sauki dole yan kasuwar zasu yi kasa da farashin su.

An dai fara yada jita-jitar yiwuwar tashin farashin man fetur a kasar nan inda wasu ke cewa hakan zai faru sanadiyyar tsadar da danyen mai yayi a kasuwar duniya.

Wasu alkaluma sunce tuni wasu defo-defo, na yan kasuwa suka kara farashin fetur a farkon wannan mako zuwa naira 960, ko 950, da haka ke nuni da yiwuwar tashin farashin man zuwa naira 1,050.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here