Rundunar yan sandan jihar Benue ta sanar da mutuwar wasu iyalai 9, sakamakon wata babbar motar data afka har cikin gidan su bayan ta kwace daga hannun direban ta, a kauyen Okete, dake karamar hukumar Otukpo.
:::Matatar Dangote ta ragewa matatun fetur na Turai ciniki—OPEC
Mai agana da yawun rundunar CSP Sewuese Anene, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a yau alhamis.
Yace mummunan lamarin ya faru a yau alhamis da sanyin safiya.
Rundunar yan sandan tace zata tsaurara bincike akan hatsarin, da kuma yin karin haske a nan gaba kada.