Gobara ta kone wani babban Otal a birnin Abuja

0
43

Wata gobara data tashi tayi sanadiyyar konewar Otal din Focus Holiday Inn, dake Garki, a birnin tarayya Abuja.

Ma’aikatan Otal din sun ce wani bako da ya zo ne ya sanar da su tashin wutar bayan ya zo wajen ma’aikatan a wajen karbar baki.

Rahotanni sunce wutar data fara tashi daga hawa na 3, ta bazu cikin sauri zuwa wasu sassan da hakan ya jefa firgici a zukatan mutanen da suka kama dakuna a Otal din na Focus Holiday Inn.

Majiyar jaridar Vanguard, tace jami’an kashe gobara basu halarci wajen akan lokaci ba duk da kiran gaggawar da aka yi musu.

Otal din Focus Holiday Inn, an samar dashi a shekarar 2022, kuma ya zama daya daga ciki Otal mashahurai a Abuja.

Kawo yanzu dai ba’a san dalilin tashin gobarar ba, saboda har yanzu ba’a samu wani karin bayani daga mamallaka Otal din ko ma’aikatan sa ba, kuma ba’a samu labarin asarar rai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here