CBN ya ci bankuna 9 tarar naira biliyan 1.35, saboda kin saka kudi a ATM lokacin Kirsimeti

0
62

Babban bankin kasa CBN yaci wasu bankuna 9, tarar kudi har naira biliyan 1.35, bisa samun su da gazawa wajen samar da isassun kudi a na’urar cire kudi ta ATM, lokutan bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

Bankin CBN yace kowanne banki daya zai biya tarar naira miliyan 150, saboda karya dokar rarraba kudi, bayan an gudanar da bincike akan kowanne banki don sanin yanda suka yi hada-hadar kudade lokacin bukukuwan.

:::Hatsarin mota ya kashe manoma 7 a jihar Niger

Mai rikon mukamin daraktan yada labarai na bankin Hakama Sidi Ali, ce ta sanar da hakan inda tace CBN, ba zai lamunci kawo wasa a wadatuwar tsabar kudi a hannun al’umma ba, saboda hakan yana da muhimmanci ga fannin inganta tattalin arziki, da samun yardar al’umma.

Bankunan da aka ci tarar kudin sun hadar da Fidelity, First Bank, Keystone, Union, Globus, Providus, Zenith, UBA, da kuma Sterling Bank.

CBN, yace kai tsaye zai yanke tarar daga asusun bankunan.

Haka zalika CBN, yace zai cigaba da bibiyar cibiyoyin hada-hadar kudi don saukakawa mutane karancin kudi da suke fuskanta, musamman a bankuna da masu POS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here