Gwamnatin tarayya ta kara kudin ciyar da daurarrun gidan yari

0
19

Gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin abincin da take kashewa kowanne daurarren gidan yari, daga naira 750, zuwa 1,125, a kowacce rana.

An kara kudin sakamakon yadda ake samun hauhawar farashin kayayyakin masarufi, da hakan ya sanya ake samun gibin wadanda abincin baya isa gare su.

:::Cire tallafin man fetur alheri ne ga gwamnoni—Gwamnan Jihar Imo

Mai rikon mukamin shugaban kula da gidajen gyaran hali na kasa Sylvester Ndidi Nwakuche, ne ya sanar da hakan lokacin da yake zantawa manyan jami’an hukumar kula da gidajen gyaran halin, yana mai cewa hakan ci gaba ne, amma akwai bukatar kara inganta ciyarwar.

Yace duk da haka zai cigaba da neman gwamnatin Tinubu, ta sake inganta tsarin ciyar da fursunonin duk da cewa a yanzu ma gwamnatin tayi kokari.

Sylvester Ndidi Nwakuche, yace an samar da wata tawagar musamman wadda zata sanya idanu akan cewa ana ciyar da fursunonin yanda ya kamata, ba tare da samun tangarda ba.

Mukaddashin shugaban kula da gidajen gyaran halin yace a yanzu haka akwai fursunoni 48,932, dake jiran shari’ah, daga ranar 6, ga watan da muke ciki, wanda yace zai hada hannu da ma’aikatar shari’a ta tarayya, da masu ruwa da tsaki, da kuma shugaban yan sandan kasa don yankewa wadanda ke jiran shari’ar hukunci cikin gaggawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here