Kamfanoni 250 sun samarwa kansu lantarki megawatt 6500 saboda lalacewar wutar Nigeria

0
71

Yawan dauke wutar lantarkin da ake samu ya saka kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin hada-hada fiye da 250, sun samarwa da kansu wutar lantarki ta hanyar yin amfani da kamfanonin su masu rarraba lantarkin.

Kamfanonin wanda suke yin amfani da wutar lantarki mai yawan gaske saboda girman injinan da suke amfani da su sun jingine batun dogaro da babban turken wutar lantarkin kasar nan, don samarwa da kansu wutar da take da tabbas.

Hakan yazo a daidai lokacin da farashin lantarkin ke kara yin tsada tare da fuskantar tashin farashin fetur, da yawan lalacewar babban turken wuta da sauran kalubale da tabarbarewar harkokin makamashi.

:::Kanfanonin jiragen sama 4 ne zasu yi jigilar maniyyatan Nigeria zuwa Saudiyya-NAHCON

A shekarar 2021, tsohon shugaban Nigeria Obasanjo, ya jingine yin dogaro da wutar lantarkin da Nigeria ke samarwa, inda ya koma yin amfani da wutar daya samar mai karfin megawatt 2, da take yin amfani da hasken rana, a babban dakin karatu dake Abeokuta dake Ogun.

Tun a wancan lokaci Obasanjo, yace aikin samar da wutar mai amfani da rana sai da ya lakume naira biliyan 2, yana mai cewa duk da haka akwai amfanuwa a wutar.

Wasu alkaluman da aka samo daga hukumar kayyade farashin lantarki ta kasa NERC, ya nuna cewa kamfanoni sun samarwa da kansu wutar lantarki mai karfin megawatt 6500, wadda ko gwamnatin Nigeria bata taba samar da wuta mai wannan karfi ba, inda take samar da megawatt 4000, ko 4500.

Haka zalika bincike ya nuna cewa hukumar NERC, ce ta bawa kamfanonin damar samarwa kansu lantarki, wanda aka fara bayar da damar daga shekarar 2020, zuwa 2022.

Kamfanin Dangote, shine yafi kowanne samarwa kansa lantarki, wanda ya samar da wuta mai karfin megawatt 1500, sai matatar sa data samarwa kanta wuta ai karfin megawatt 435.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here