Gwamnatin Borno ta tabbatar da kisan manoma 40

0
32

Gwamnatin jihar Borno, ta tabbatar da kisan wasu manoma 40, a karamar hukumar Kukawa.

Daily Trust, ta rawaito cewa, harin ya faru a ranar lahadin data gabata, wanda ake zaton cewa mayakan Boko Haram, ne suka kashe manoman, da masu kamun kifi.

:::Nigeria zata toshe hanyoyin da Boko Haram ke samun kudade daga ketare

Kwamishinan yada labaran Borno, Farfesa Usan Tar, ya bayyana lamarin a matsayin ta’addanci, lokacin da yake tabbatarwa da manema labarai harin.

Yace gwamna Babagana Zulum, yayi ala wadai da kai harin sannan ya roki sojoji su binciko tare da hukunta maharan.

A jiya lahadin yan ta”addan da ake zaton yan Boko Haram/ISWAP, ne suka kaiwa manoman da masu kamun kifi hari a yankin Dumba, a kusa da Baga dake karamar hukumar Kukawa.

Tar, yace zuwa wannan lokaci an fara gudanar da binciken maharan, wanda aka gano cewa an kashe mutane 40, sannan ana kan hanyar lalubo sauran wadanda suka tserewa harin don hada su da iyalan su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here