Bama kai hari da niyyar kashe fararen hula—Sojin Nigeria

0
74

Hafsan hafsoshin kasa Janar Christopher Musa, yayi bayanin cewa dakarun su suna bin tsauraran matakai kafin kaddamar da wani harin jiragen sama a duk yankunan da suke yakar yan ta’adda.

:::Kamfanoni 250 sun samarwa kansu lantarki megawatt 6500 saboda lalacewar wutar Nigeria

Musa, ya kara da cewa sojojin suna kai hari akan ka’ida da daidaito, kuma basu taba yin niyyar kaiwa fararen hula hari da jirgi ba.

Hafsan Hafsoshin, ya sanar da hakan ne a yau litinin, lokacin da ake zantawa dashi ta kafar yada labarai ta Arise, akan yadda jirgin yakin kasar nan ya kashe yan sa kai 16, a jihar Zamfara, lokacin da mutanen ke kokarin kai dauki ga wasu al’ummar da yan ta’adda suka kaiwa hari.

Ya kare rundunar sojin da cewa tabbas basa taba kai wani hari sai sun bi ka’ida da kuma yin amfani da kwarewa, inda yace hari na biyu da suka kai a Zamfara, an kai shi ne ga wajen ajiye makaman yan ta’adda, tare da cewa wannan hari ne zai iya shafar fararen hula.

Musa, yace wajen ajiye makaman na dauke da bama-bamai, wanda in suka tashi zasu iya kaiwa ga mutanen dake kusa da ma’ajiyar, sannan yace babu wani abun da yayi kama da cewa sojoji sun kai harin don kashe fararen hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here