Tsohon kwamishinan Kano ya fice daga NNPP zuwa APC

0
45

Kalubalen sauyin shekar siyasa na cigaba da daukar sabon salo a siyasar jam’iyyar NNPP, a daidai lokacin da Hon. Abbas Sani Abbas, ya fice daga jam’iyyar zuwa APC, a matakin jihar Kano.

Abbas, ya kasance tsohon kwamishinan raya karkara, na jihar Kano, daga farkon gwamnatin Abba, zuwa watan daya gabata, inda ya sanar da ficewar sa daga NNPP, a jiya Juma’a, lokacin daya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I Jibril.

Jaridar, Daily trust, ta rawaito cewa a watanni 6, da suka gabata dubban mabiya NNPP, sun fice daga cikin ta zuwa APC, a kananun hukumomin jihar Kano 44.

Abbas Sani Abbas, yace zai yi tafiyar siyasa bisa son cigaban APC da samun nasarar ta a Kano da kasa baki daya.

Shima mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I Jibril, ya bayyana Abbas Sani Abbas, a matsayin dan siyasa tun daga tushe, wanda zai yi aiki don samun nasara a jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APC, na Kano Abdullahi Abbas, ya ziyarci wajen karbar tsohon kwamishinan.

Abbas Sani Abbas, na daga cikin kwamishinonin da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya kora biyo bayan garambawul a fannin majalisar zartarwa ta jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here