Cinikin dabbobi tsakanin kudu da arewacin Nigeria ya ragu da kaso 50

0
28

Masu sana’ar siyar da shanu na fuskantar barazanar daina yin Sana’ar tasu musamman daga arewacin Nigeria, zuwa kudu a daidai lokacin da masu ruwa da tsaki ke kiran a kawo wa masu yin harkar dauki don hana su durÆ™ushewa.

Binciken da jaridar Daily trust, ta gudanar ya bayyana cewa karuwar ayyukan ta’addanci, da haramta kiwon sakin dabbobi barkatai a sassan kasar nan, ba tare da daukar matakan samarwa makiyaya mafita ba, na daga cikin manyan dalilan dake kawo barazanar durÆ™ushewar fannin kiwo, wanda haka ya tilastawa mafi yawancin makiyaya yin kaura daga Nigeria zuwa makwabtan kasashe irin su Niger, Kamaru, Chadi, Sudan, da l Afrika ta tsakiya.

Wakilin Daily trust, da ya ziyarci jihohin Arewa maso gabas, ya samu damar zantawa da masu ruwa da tsaki a harkar kiwo, wanda suka sanar da shi cewa suna cikin kuncin yanda harkokin su suka lalace.

Wasu alkaluman da aka tattara sun nuna cewa a cikin watanni 6 da suka gabata a kasuwannin dabbobi 63 dake yankin arewa maso gabas, an tashi motocin dabbobi 593, zuwa kudu, a kowacce rana.

Haka ya nuna cewa kowacce motar trailer tana daukar shanu 42, wanda lissafi ya tabbatar da cewa yawan dabbobi da ake kaiwa kudu musamman Lagos, Enugu, Port Harcourt, Akwa Ibom, Onisha, Uyo, da sauran su, sun kai 25,499, Kuma hakan kadan ne idan aka kwatanta da baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here