Shugaban Nigeria Tinubu zai tafi kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

0
64

Shugaban kasa Bola Tinubu zai tafi ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa domin halartar taron ɗorewar tattalin arziki na duniya na shekarar 2025.

Shugaban ƙasar, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci shugaba Tinubu domin halartar taron wanda zai gudana tsakanin 12 zuwa 18 ga watan Janairu.

Taron zai samu halartar manyan shugabannin duniya, da masana da ƙungiyoyin fararen hula da ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki.

Yayin taron za’a tattauna nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki da zamantakewa, tare da lalubo hanyoyin ɗorewar ci gaban da aka samu.

Cikin sanarwar da fadar shugaba Tinubu, ta fitar, ta ce a taron Shugaba Tinubu zai jaddada manufofin gwamnatinsa, ciki har ci gaban tattalin arziki da makamashi da sufuri da fannin lafiya.

Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, na daga cikin manyan jami’an gwamnatin da za su yi wa shugaban rakiya.

Ana sa ran shugaban zai koma Najeriya bayan kammala taron ranar 16 ga watan Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here