Wutar daji ta kashe mutane 5 da kone gidaje dubu 2 a birnin Los Angeles na Amurka

0
30

Wata mummunar gobarar wutar daji tayi sanadiyyar mutuwar mutane 5, tare da kone gine gine akalla dubu 2, a birnin Los Angeles na Amurka.

A yanzu haka ana kan hanyar cigaba da aikin kwashe mutane da yawan su yakai dubu dari daga guraren da ake zaton wutar zata iya kaiwa nan da kankanin lokaci.

Wutar dajin wadda ta kwashe tsawon lokaci tana ci ta kone fadin kasa mai girman Eka 15,800,

Wutar da yi karfi da misalin karfe 5:45 agogon Amurka, yayin da take cigaba da ruruwa a unguwar Hollywood Hills.

Zuwa wannan lokaci al’amura sun tsaya cak musamman kasuwanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here