Kotu ta bayar da belin Mahadi Shehu

0
53

Babbar Kotun jihar Kaduna, ta bayar da belin Dan Gwagwarmaya Mahadi Shehu, wanda jami’an tsaro suka kama kwanakin baya.

Kotun dake karkashin mai shari’a Murtala Zubairu, ce ta bayar da belin dan Gwagwarmayar, bayan tsarewar da aka yi masa a gidan yarin Kaduna bisa zargin sa da fitar da wani faifan bidiyon dake nuna cewa sojojin Faransa suna aiki a wasu sannan Nigeria.

Fitar da faifan bidiyon yazo bayan da shugaban kasar Nijar na mulkin soji, ya zargi Nigeria, da hada kai da kasar Faransa, don haifar da rashin tsaro a Nijar da wasu kasashen Afrika.

Shugaban na Nijar, yace akwai dakarun Sojin Faransa dake zaune a wasu yankunan Nigeria, kuma ana shirin yin amfani da Nigeria, don kawo cikas ga al’amuran Nijar.

Sai dai gwamnatin Nigeria, ta musanta zargin da Nijar tayi, wanda ana tsaka da yin wannan turka-turka Mahadi Shehu, ya fitar da faifan bidiyon dake nuna zargin tabbas akwai sojojin Faransa a Nigeria, kuma wannan abu ne yasa aka kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here