Jami’an tsaro sun kubutar da mutum 63 da aka sace a Sokoto

0
55

Jami’an tsaro a jihar Sokoto, sun kubutar da wasu mutane 63, da yan ta’adda sukai garkuwar dasu, domin karbar kudin fasar su daga wajen iyalan wadanda aka sace din.

:::Faransa ce barazanar zaman lafiyar kasashen Afrika–Tsohuwar Wakiliyar AU

Mataimakin Gwamnan jihar Garba Mohammed, ne ya sanar da hakan cikin wata sanrwar daya sakawa hannu, yana mai cewa jami’an da suka samu nasarar wannan aiki sun hadar da yan sanda da sauran jami’an tsaron dake aiki a Sokoto.

A ranar lahadi data gabata ne aka ceto mutanen.

Jihar Sokoto, na daya daga cikin jihohin arewa masu fama da ayyukan yan ta’adda masu kashe mutane babu dalili tare da sace dabbobi da kuma sace dan adam domin karbar kudin fansa, wani lokacin ma su karbi kudin fansar sannna su hallaka mutum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here