Faransa ce barazanar zaman lafiyar kasashen Afrika–Tsohuwar Wakiliyar AU

0
32

Tsohuwar Wakiliyar kungiyar tarayyar Afrika (AU) a Amurka, Arikana Chihombori-Quao, tace kasar Faransa ce babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron nahiyar Afirka.

Arikana ta bayyana haka ne a hirar ta da kafar yada labarai ta TRT Afrika, domin yin raddi ga kalaman da shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi na cewa ƙasashen Afirka basu da godiyar Allah.

Macron, yace sojojin kasar sa sunyi aiki tukuru don samar da zaman lafiya a kasashen Afrika, amma duk da haka basa godewa kasar tasa sai dai zargin ta da suke yi.

Yace kasar Faransa itace ta taimakawa kasashen Afrika har suka kai ga samun yanci daga mulkin mallakar da ake yi musu a baya.

Sai dai masana harkokin yau da kullum, suna kallon Faransa, a matsayin mai take karfin nahiyar Afrika, da hana su cigaba, musamman wadanda ta yiwa mulkin mallaki irin su, Chadi, Niger, Burkina Faso, da sauran su, da a yanzu suke nuna yatsa ga Faransa, har wasu daga cikin su ke neman yanke huldar diflomasiyya da ita.

Shima shugaban Ć™asar Nijar, na mulkin soji ya zargi Faransa da hannu wajen dagula al’amuran tsaro a yankin Sahel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here