‘Yan ta’adda sun sace mutane 46 a jihar Zamfara

0
69

Sha’anin tsaro na kara samun koma baya a wasu yankunan arewacin Nigeria a daidai lokacin da yan ta’adda ke kara jefa zulumi da fargaba a zukatan al’ummar yankunan da ake samun matsalolin tsaron.

Idan akayi batun lalacewar harkokin tsaro a Nigeria dole tunanin mutun zai koma kan yankin arewa, musamman jihohin arewa maso gabas da arewa maso yamma.

A halin yanzu dai an samu wasu bata gari da suka sace mutane 46, a jihar Zamfara, da take daya daga cikin jihohin da matsalar tsaron ta dabaibaye.

:::Shugaban NNPCL ya nemi yafiyar wadanda ya batawa rai

Lamarin ya faru a garin Gana da ke jihar ta Zamfara.

An sace mutanen ne a yayin da ɗan fashin daji Dogo Giɗe, ya sanyawa wasu garuruwa 23 a ƙaramar hukumar tsafe, harajin naira miliyan 100 bisa sharaɗin kai musu hari matuƙar suka gaza haɗa adadin kuɗin da ya nema.

Amma mazauna yankin sun shaidawa RFI, cewa ba’a yi musu wannan barazana ba.

A cikin ranakun karshen makon daya gabata ne yan ta’adda masu yawa suka kaiwa garin na Gana hari, wanda suka kone gidaje tare da sace mutane cikin su har da mata da kananun yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here