ICPC ta kai karar tsohon gwamnan Kaduna El-Rufa’i akan zargin rashawa

0
50

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da dangogin su ta kasa ICPC ta kai karar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon kwamishinan sa, Bashir Sa’idu gaban kotu kotu bisa zargin su da almundahanar kuɗaden gwamnatin jihar a zamanin mulkin sa.

Jami’in sashin shari’a na hukumar ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ne ya gabatar da ƙarar ga babbar kotun tarayya da ke Kaduna a jiya Talata.

Takardar ƙarar mai lamba FHC /KD/IC/ 2025, ta nuna cewa an shigar da El-Rufai da Bashir Saidu, kara a gaban kotun bisa tuhume-tuhume guda biyu da suka danganci almundahana da rashawa.

A wani rahoto da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar a shekarar data gabata, ta zargi tsohon gwamnan da almundahanar sama da naira biliyan 423 na jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here