Shan lemon kwalba mai zaki sosai ka’iya haddasawa mutum mutuwa—Bincike

0
83

Wani binciken Cibiyar Nazari ta Nature Medicine, yace aƙalla mutane 330,000 ke mutuwa a duniya sakamakon cututtukan da suke kamuwa dasu ta hanyar shan lemukan kwalba masu zaƙi sosai.

Labarin da shafin Hausa na BBC, ya wallafa yace, a cikin cututtukan, da lemon yafi haddasawa akwai ciwon suga da kuma cututtukan da suka shafi zuciya.

Bayan haka shan lemon kwalba mai dauke da sinadaran Citric acid ko gas na iya kawo cikas ga lafiyar masu fama da matsalolin da suka shafi ciki, irin su gyambon ciki, basir da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here