Wata sabuwar cuta mai kama da Corona, HMPV ta bulla a kasar China da India

0
26

Kasar China tana ci gaba da fuskantar karuwar masu fama da wata cutar numfashi mai saurin yaduwa mai suna HMPV.

Lamarin ya kawo cunkoson marasa lafiya a wasu asibitocin kasar, da sauran cibiyoyin kula da lafiya.

Bayan kasar China, an bayar da rahoton cewa yanzu haka an samu mutanen da suka kamu da cutar ta HMPV a kasar India.

Cutar HMPV ta bulla shekaru biyar bayan duniya ta yi fama da annobar Cutar Coronavirus wacce ta yi ajalin mutum fiye da miliyan bakwai.

Itama dai Cutar Corona idan ba’a manta ba ta samo asali daga birnin Wuhan na kasar China.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here