Tsaffin gwamnonin Kano su hada kai domin samun cigaba—Murtala Garo

0
78

Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023, Murtala Sule Garo, ya roki tsaffin gwamnonin Kano su hada kai tare da mantawa da banbance banbancen siyasar dake tsakanin su don samarwa jihar cigaba.

Garo, ya bayyana hakan a lokacin da aka shirya liyafar cin abinci karkashin jagorancin kungiyar yan majalisar dokikin Kano, ta majalisa ta 8,9, da 10, inda yace tabbas hadin kan tsaffin gwamnonin Kano yana da alfanu wajen cigaban jihar.

Yace abin takaici ne ace jihar Zamfara wadda bata kai jihar Kano cigaba ba, tsaffin gwamnonin ta sun hada kai sun yi watsi da banbancin siyasar su inda suka mayar da hankali wajen sanarwa jihar su mafita dangane da kalubalen da take ciki.

Garo, yace yana kira ga manyan yan siyasar dasu sanya wata alkibla daya a gaba ta son cigaban Kano, saboda wannan ne zai zamar mana alkairi, samar da cigaban al’ummar mu.

Dan takarar mataimakin gwamnan, yace in har da gaske tsaffin, gwamnonin suna kaunar cigaban Kano ya zama wajibi su hade guri guda, saboda cigaba baya samuwa a irin wannan hali da yan siyasar Kano ke ciki.

Alhaji Murtala Garo, ya jinjinawa, wadanda suka shirya taron liyafar cin abincin musamman akan yadda suka hada kai waje guda. Sannan yace in aka yi koyi da halin mambobin kungiyar Kano zata samu cigaba.

Taron ya samu halartar fitattun yan siyasar APC, da masu ruwa da tsaki, musamman a yanzu da jam’iyyar ke shirin tunkarar zaben shekarar 2027, don dinke barakar dake damun ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here