Kotu ta bayar da belin matar da tayi barazanar kashe dan shugaban yan sandan Nigeria

0
18

Wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja, ta bayar da belin wata mata mai suna Olamide Thomas, da tayi barazanar kashe shugaban yan sandan kasa Egbetokun, tare da dan shugaban kasa Seyi Tinubu.

Kotun tace matar zata biya kudin beli naira miliyan 10 da kuma nemo wanda zai tsaya mata, biyo bayan barazanar kisan da ta yiwa mutanen biyu a kafar sada zumunta.

Mai shari’a Emeka Nwite, ne ya bayar da belin Olamide Thomas, yana mai cewa babu wata hujjar da zata hana bayar da belin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here