Fashewar tankar mai ta kashe mutane 4 da konewar bankuna 2

0
70

Konewar wata tankar mai da ta kama da wuta tayi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da konewar wani banki da wasu gine gine a karamar hukumar Ika ta Kudu dake jihar Delta.

Lamarin ya faru a yankin Agor, a ranar lahadi data gabata, lokacin da motar ke tafiya a tsohuwar hanyar Lagos zuwa asaba, inda motar man ta fadi a kusa da wani reshen First Bank, sannan ta kama da wuta.

Mutane da dama sun jikkata baya ga asarar rayuka dukiyoyi a hatsarin.

A cewar shaidu, hatsarin ya auku ne a yayin da direban motar yake ƙoƙarin juyawa a kusa da reshen bankin da ke Agbor.

Wani ganau ya ce bankuna biyu da wasu gine-gine sun kama da wuta baya ga mutanen da aka yi asarar.

Gwamnan Jihar Delta, Sherif Oborovwori, ya mika ta’aziyya game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here