Gwamnatin Gombe zata biya tsaffin ma’aikata hakkin su har naira biliyan 19

0
23

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Yahaya, ya kara jaddada aniyar sa ta biyan tsaffin ma’aikatan jihar hakkin su na garatuti.

Yahaya, yace tuni gwamnatin sa ta biya naira biliyan 17.2 ga ma’aikatan da suka yi ritaya a lokacin gwamnatocin baya, wanda suka bar masa bashin biyan ma’aikatan hakkin su har naira biliyan 21.

Yahaya, ya bayyana hakan a yau litinin, lokacin da yake mika shaidar karbar kudi a banki ga tsaffin ma’aikatan yana mai cewa gwamnatin sa ta damu wajen inganta walwalar ma’aikata.

A cewar sa lokacin daya karbi mulkin jihar Gombe, a shekarar 2019, ya samu tsaffin ma’aikatan suna bin bashin naira biliyan 21, amma kawo yanzu ya biya naira biliyan 17.2, na adadin kudaden.

Yace yanzu haka ana bin jihar naira biliyan 19, na garatuti wanda ya hadar da hakkin tsaffin ma’aikatan jihar dana kananun hukumomi, inda yace tabbas zai yi kokarin biyan wadannan kudade baki daya kafin shekarar 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here