Al’ummar Kano zasu yi Azumin Ramadan cikin wadatar ruwan Famfo—Gwamnatin Kano

0
52

Gwamnatin jihar Kano, tace ya zama wajibi ma’aikatun gwamnati da kamfanoni su riƙa biyan kuɗin ruwan famfon da suke yin amfani da shi.

Kwamishinan ruwa Umar Haruna Doguwa, ne sanar da hakan a wani shiri na gidan radiyon Kano, da aka gudanar a daren ranar Asabar.

Doguwa, yace daga yanzu za’a fara karɓar kuɗin ruwan famfo daga ma’aikatun gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su a fadin jihar, ba tare da wasa ba.

Yace bai dace ba ma’aikatun gwamnati su riƙa amfani da ruwa kyauta, saboda gwamnati tana basu kudin gudanarwa a kowanne wata.

Doguwa, yace manyan kamfanoni ma sai sun riƙa biyan kudin ruwa duk wata.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin za ta duba yiwuwar yin ragin kuɗin ruwa ga al’ummar jihar.

Doguwa ya tabbatar da cewa zuwa watan Yuni na bana ruwa zai wadata a jihar Kano sakamakon goyon baya da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ke baiwa ma’aikatar ruwa.

A cewar sa, akwai wasu injinan tunkudo ruwa, wanda su ka lalace saboda tun lokacin tsohuwar gwamnatin Kwankwaso, ake yin amfani da su

Amman yace gwamnan Kano ya bada umarnin a sayo sabbi a saka, inda ya ce al’ummar Kano za su yi Azumin Ramadan cikin wadatar ruwan famfo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here