Wasu yankunan Abuja zasu shafe makonni babu lantarki

0
67

Kamfanin rarraba wutar lantarki reshen birnin tarayya Abuja, AEDC ya ce wasu sassan birnin za su fuskanci daukewar lantarki ta tsawon makonni biyu.

AEDC ya sanar da haka a jiya Juma’a a shafin sa na X, inda ya ce za a fara fuskantar rashin wutar daga ranar Litinin mai zuwa.

Sanarwar ta ce hakan zai faru sakamakon gyara da kuma komawa zuwa babban layin ba da wuta na megawatt 33 da kuma layin da ke bayar da wuta na megawatt 132 da ke Kukwaba.

A cewar kamfanin, za a yi aikin komawa babban layin ne daga ranar Litinin 6 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan.

Yankunan da zasu fuskanci rashin wutar sune Lugbe da Airport Road da Kapwa da NNPC da Games Village da kuma National Stadium.

Sauran sun haÉ—a da Gudu da Gbazango da sassan Kubwa da Bwari da Jahi da sassan Jabi da Karu da Nyanya da Mararaba da kuma Keffi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here