Hukumar tace tace fina finai ta Kano ta dakatar da Sahma M. Inuwa

0
27

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano, ta dakatar da jaruma Sahma M Inuwa, daga shiga harkar film, ta tsawon shekara daya, tare da kwace shedar ta, ta zama halastacciyar jarumar film.

Hukumar ta sanar da haka cikin wata sanarwar data fitar mai dauke da sanya hannun jami’in yada labaran ta Abdullahi Sani Sulaiman.

Hukumar ta sha al’washin kin tace duk wani film da Samha ta fito a ciki.

Hukumar tace aukar matakin ya biyo bayan wasu korafe korafe da al’umma suka yi kan wani faifan bidiyo da jarumar ta saki dake nuna shigar da bata dace da koyarwar addinin musulunci ba, baya ga samunta da yin kalaman da basu dace ba.

Ya zuwa yanzu dai Hukumar ta dakatar da Samha har tsawon shekara daya a wani mataki na tabbatar da bin dokokin Hukumar tare da kara tsaftace Masana’antar kannywood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here