Gwamnan jihar Nassarawa ya sauke baki dayan kwamishinonin sa da masu bashi shawara

0
112

Gwamna Nassarawa, Abdullahi Sule ya sauke ɗaukacin kwamishinonin sa tare da Sakataren Gwamnatin Jihar.

Bayan haka gwamnan ya sauke dukkanin masu bashi shawara.

Gwamna, Sule, ne ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa daya gudanar a gidan gwamnatin jihar Nassarawa dake Lafia a yau Juma’a.

Ya sanar da daukar matakin korar yan majalisar zartarwar tasa ne jim kadan bayan tafiyar mataimakin shugaban kasa Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana daya a jihar domin kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

Kawo yanzu dai ba’a bayyana cikakken dalilin dauke masu rike da mukaman ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here