Dangote ya ƙulla wata yarjejeniyar karya farashin man fetur

0
33

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙulla wata yarjejeniya da kamfanonin Heyden, da Ardova, don samar da man fetur a farashi mai sauki a kasar nan.

Matatar ta sanar da hakan ne a jiya alhamis, inda aka yi yarjejeniyar cewa kamfanonin zasu rika siyan tataccen fetur mai yawa daga Dangote, tare da samun tallafin siyan danyen mai da takardar kudi ta Naira.

Sanarwar da kamfanin Dangote, ya fitar tace, hakan baya rasa nasaba da kokarin sa na inganta kasuwar man fetur, da taimakawa fannin samar da makamashi a Nigeria.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ma matatar Dangote, ta sanar da hada gwuiwa da kamfanin MRS, don siyarwa mutane fetur, a farashin naira 935.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here