Tinubu ya kwashe kwanaki 180 a kasashen ketare bayan hawan sa mulkin Nigeria—Peter Obi

0
40

Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar LP, a zaben shekarar 2023, Peter Obi, yace shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya kwashe kaso 30, na adadin kwanakin da yayi akan karagar mulki a kasashen waje.

Daga lokacin da Tinubu, ya hau mulkin Nigeria zuwa ranar 29, ga watan Disamba na shekarar data gabata, yayi kwanaki 580, a mulkin kasar, inda yayi kwanaki 180, ba a Nigeria ba.

Obi, ya bayyana hakan a yau lokacin da ake zantawa dashi a birnin tarayya Abuja, yana mai cewa a shekarar da muke ciki 2025, Nigeria tana bukatar shugaban da zai sadaukar da kansa ga cigaban ta.

Daga shekarar da aka rantsar da Tinubu, zuwa yanzu ya ziyarci kasashen da suka kai 16.

Kasar Faransa, na daga cikin Kasashen da yafi zuwa, bayan samun mulkin Nigeria.

Masana harkokin yau da kullum na ganin cewa Nigeria tana bukatar shugaban da zai mayar da hankali wajen inganta cigaban ta yayin da take fuskantar kalubalen tsaro, tattalin arziki, rashin aikin yi, da tsadar rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here