Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado, ya dawo Nigeria bayan ziyara a kasar Masar

0
89

Wasu daga cikin al’ummar jihar Kano,sun tarbi Mai Martaba Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, a filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa na Aminu Kano, Bayan dawowar sa daga kasar Egypt a wata ziyarar ya kai.

Masoyan sarkin sun nuna farin cikin su, da dawowar sa a lokacin da suka tarbe shi.

Al’ummar da suka tarbi sarkin sun yi masa rakiya har zuwa gidan sarki na Nassarawa dake kwaryar birnin Kano.

Idan dai za’a Iya tunawa Kimanin makonni biyu Kenan Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bar jihar Kano zuwa kasar ta Masar.

A lokacin ziyarar ne Alhaji Aminu Ado Bayero, ya karbi bakuncin kungiyoyi daban daban na yan Najeriya, mazauna kasar.

Bayan saukar sa a fadar sa dake Nassarawa Mai Martaba Sarkin Kano, na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya godewa al’ummar da suka tarbe shi tare da yi musu fatan alheri.

Alhaji Aminu Ado Bayero yayi amfani da wannan dama wajan Kara Jan hankali matasa su cigaba da kasancewa masu da’a da ladabi da biyayya da son junansu da Kuma Zaman lafiya, kamar yadda sakataren yada labaran sa,
Abubakar Balarabe Kofar Naisa, ya sanar cikin wata sanarwa daya fitar a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here