NNPC ne suka hana Dangote damar gyara matatun fetur na Nigeria a shekarar 2007—Obasanjo

0
58

Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, yace kamfanin mai na NNPC, ne yaki amincewa attajirin Africa Alhaji Aliko Dangote, damar gyara matatun man fetur din Kaduna da Fatakwal, a shekarar 2007.

Obasanjo, yace Dangote, ya mikawa NNPC bukatar sa ta kula da matatun, wanda shi kuma zai bawa kamfanin kudin da yawan su yakai dala miliyan 750.

Tsohon shugaban ya sanar da haka a lokacin da yayi wata zantawa da tashar talbijin ta Channels, inda yace an sauya fasalin NNPC zuwa NNPCL, kuma duk da haka ba zasu iya kula da matatun man fetur din Nigeria kamar yadda Dangote, yayi niyyar yi a baya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here