Yawan al’ummar Nigeria zai haura mutane miliyan 237 a shekarar 2025

0
51

Wani kiyasi da majalisar dinkin duniya tayi yace adadin al’ummar da ke rayuwa a Nigeria, zai kai mutane miliyan 237,527,782, a shekarar 2025.

Bayanin hakan ya fito cikin wani rahoton majalisar dinkin duniyar, inda tace adadin zai haura wanda ake dashi a watan Disamba na 2024, da Nigeria ke da yawan al’umma 235,072,214 .

:::Kasar Newzealand ta shiga sabuwar shekarar 2025

Kididdiga ta zayyana cewa an samu karin mutane miliyan 4,796,533, a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024.

Wannan jawabi yazo a daidai lokacin da cibiyar kidayar al’umma ta Amurka, a ranar litinin ta sanar da cewa a cikin shekarar 2024, duniya ta samu karuwar al’umma da mutune miliyan 71, wanda aka samu koma baya sabanin shekarar 2023, da aka haifi mutane miliyan 75.

Binciken na majalisar dinkin duniya ya kara da cewa Nigeria itace ke dauke da kaso 2.85, na yawan al’ummar dake rayuwa a duniya, kuma itace kasa ta 6, a jerin kasashen da suka fi yawan al’umma.

A yadda bayanin rahoton ya nuna jihar Legas ce tafi yawan al’umma a Nigeria da mutane 15,388,000, sai Kano mai mutane 4,910,000.

Daga Karshe ana kyautat zaton yawan al’ummar duniya zai kai mutum biliyan 8.09, a gobe daya ga watan Junairun 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here