Yan Nigeria 326 ne suka rasu a shekarar 2024 sakamakon hatsarin jirgin ruwa

0
43

Akalla yan Nigeria 326, ne suka rasa rayukan su a shekarar 2024, bayan da suka gamu da iftila’in hatsarin jirgin ruwa, ko kwale kwale.

Jaridar The Cabel, ta rawaito cewa lamarin mutuwar mutane a jirgin ruwa ta kazanta a kasar nan in aka kwatanta da shekarar 2023.

Lamarin sifurin jirgin ruwa ya zama tamkar wata hanyar mutuwa, musamman a yankunan kauyuka, wanda hakan ke sawa dimbin mutane suke rasa rayuwar su, saboda rashin kyakkyawan tsarin kula da lafiya a fannin.

:::Gwamnan Rivers ya gabatar da kasafin jihar ga yan majalisa 3

The Cabel, tace rashin daukar mataki daga hukumomi na kara ta’azzara yanayin lalacewar fannin sifurin jirgin ruwa, wanda hakan ke kara zama barazana ga mutanen da dole sai sunyi amfani da hanyoyin ruwa a rayuwar su ta yau da kullum.

A wannan shekara ta 2024 jihohin Kwara da Niger, ne suka fi gamuwa da hatsarin jirgin ruwan inda suka rasa mutane 90 zuwa 92, kowannen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here