Jam’iyyar PDP tace tana nan tana tsara yadda zata tuntubi tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, don ya koma cikin ta tare da yin tafiya tare don samun karfin da jam’iyyar zata iya samun nasara a zaben shekarar 2027, tare da kafa gwamnati a matakin kasa.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagun ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da BBC, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam’iyyar, PDP ta mutu, kuma ba za ta iya yin wata nasara ba a zabukan dake tafe a nan gaba.
Sai dai duk da haka Damagun, yace a shirye PDP, take wajen karbar duk wadanda suka fice daga cikin ta, inda yace har kwankwaso suna son sa ya dawo tsohuwar jam’yyar tasa.
Damagun ya ce shi kansa Kwankwason da ya ce PDP ta mutu, ai bai yi wa kansa adalci ba, domin ai ya dauki jam’iyya amma jiha nawa ya ci.