Kotu ta kwace dala dubu 49 daga hannun tsohon kwamishinan INEC

0
75

Wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta bayar da umarnin kwace dala dubu 49 da 700, da aka samu a hannun Nura Ali, wanda ya kasance tsohon kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ne da yayi aiki a jihar Sokoto, a shekarar 2023, lokacin da aka gudanar da manyan zabukan kasar nan.

Mai shari’a Emeka Nwite, ne ya bayar da umarnin kamar yadda lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya nema, don a kwace kudin na dan wani lokaci.

Gwamnatin tarayyar Nigeria itace a matsayin mai karar Ali, a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1846/2024, wanda hukumomin DSS, da ICPC, suka shigar a ranar 20 ga watan Disamba.

An samu kudaden ne lokacin da ake yin bincike akan tsohon kwamishinan wanda ake kyautata cewa ya samu kudaden ta hanyar da bata dace ba.

Bayan haka kotu ta umarci ICPC da DSS su gudanar da cikakken binciken da zai tabbatar da cewa Nura Ali, ya mallaki kudaden ta hanyar da bata dace ba, daga yanzu zuwa kwanaki 90, masu zuwa don gabatar da hujjar hakan a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here