Ya kamata a biya diyya ga wadanda sojoji suka kashe a Sokoto—PDP

0
58

Babbar jam’iyyar adawa ta Nigeria PDP ta nemi gwamnatin kasar ta biya diyya ga wadanda harin sojoji ya shafa a karamar hukumar Silame, ta jihar Sokoto, yayin da ake kokarin fatattakar mayakan Lakurawa.

Idan za’a iya tunawa a makon daya gabata ne dakaraun sojin sama suka kai wani hari ta sama don kashe lakurawa, sai dai mutanen yankunan Gidan Sama da Rumtuwa, da abin ya faru akan su sunce fararen hula sojin suka kashe ba lakurawa ba.

:::Tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter ya mutu

Wannan ne dalilin da yasa aka rika samun sabanin bayani tsakanin sojojin da al’ummar yankunan Gidan Sama da Rumtuwa, inda sojin suka ce ba fararen hula suka kashe ba, sai dai yan ta’adda, sakamakon cewa sunyi bincike kafin akai harin.

Bayan wannan mataimakin shugaban Nigeria, Kashim Shettima, ya tabbatar da kisan fararen hular cikin wani sakon jajen daya aikewa yankunan Gidan Sama da Rumtuwa, yana mai cewa ayi musu afuwa.

Jam’iyyar PDP ta nemi biyan diyyar ne a cikin sakon ta na ta’aziyya kan fararen hula da suka jikkata da waɗanda suka gamu da ajalinsu a harin jiragen sojojin.

Kakakin jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, a sanarwar da ya fitar kan harin, ya buƙaci a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano gaskiya da yin adalci.

PDP ta jaddada goyon bayanta ga taki da ta’addanci, amma ta nuna muhimmancin kula da rayukan fararen hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here