Shigo da abinci daga ketare ne zai kawo sauki a Nigeria–inji Kungiyar Manoma ta AFAN

0
73

Kungiyar manoma ta AFAN ta nemi gwamnatin tarayya da dauki matakan da zasu magance matsalolin mutuwar mutane a sanadin turmutstsun karbar tallafin abinci.

Shugaban kungiyar Kabir Ibrahim, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da talbijin ta Channels, inda yace cikin matakan da suka cancanci a dauka akwai bayar da damar shigo da muhimman abubuwan bukata na abinci daga ketare.

:::Shugaba Tinubu zai nada sabbin jakadun Nigeria na kasashen waje

Yace bayar da damar shigo da abinci ba abun so bane, amma yana da kyau a yi hakan na wani dan lokaci don samun mafita dangane da karancin abincin da ayan Nigeria ke ciki, yana mai cewa akwai aiki mai yawa da ake bukata kafin shawo kan karancin abincin.

Shugaban kungiyar ta AFAN ya kara da cewa rashin tsaro da dumamar yanayi na daga cikin kalubalaen dake haddasa koma bayan samun wadatuwar abincin, sannan ya zayyano cewa akwai bukatar samar da kayan aikin noma na zamani da suka kunshi irin shuka mai inganci, da kuma yin amfani da kimiyya da fasaha a fannin aiki gona wanda sune zasu kawo gagarumin cigaban bangaren samar da abincin.

Kungiyar AFAN ta kara da cewa dole ne yan Nigeria su rungumi noma da kuma yin sa yanda ya dace bisa hujjar cewa a kowanne lokaci ana samun karuwar yawan al’umma, wanda dole sai anyi noma yanda ya dace tare da yin noman rani don ciyar da al’ummar da kasar ke dasu ba tare da samun karancin cimaka ba.

Muna bukatar gajere da dogon shirin samar da abinci ga kasar mu, amma a yanzu da ake fuskantar mutuwar mutane saboda turmutsutsun yunwa da talauci kamata yayi mu samar da shiri mai gajeren wa’adi, don fitar da miliyoyin yan Nigeria daga yunwa, inji Kabir Ibrahim.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here