Ministan tsaro ya bayar da tallafin miliyan 10 ga wadanda harin sojoji ya shafa a Sokoto

0
81

Gwamnatin tarayya tace zata gudanar da bincike na tsanaki akan harin da sojojin Nigeria suka kai kauyukan Gidan Bisa, da Runtuwa, dake karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto, wanda harin ya kashe fararen hula 10.

Karamin ministan tsaro Bello Matawalle, ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya ziyarci Gidan gwamnatin Sokoto don yiwa gwamna Dr. Ahmad Aliyu, jajen iftila’in da aka fuskanta a jihar.

Matawalle, yace kisan mutanen babban abin takaici ne, za’a yi bincike kuma za’a yi adalci ga wadanda aka zalunta, inji ministan.

Shugaban Nigeria ya ji damuwa akan harin wanda hakan tasa shi ya umarce ni nazo nayi muku ta’aziyyar rashin da akayi, a cewar Matawalle.

Yace an kashe mutanen ne bisa samun bayanai da suka ci karo inda kafin harin aka tabbatar da cewa mayakan Lakurawa ne ke zaune a kauyukan.

Matawalle, ya bayar da kyautar naira miliyan 10, ga iyalan wadanda harin ya kashe.

A nasa jawabin gwamnan jihar Sokoto, ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su rika tantance bayanan sirri kafin kai hari don kaucewa kisan fararen hula.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here