Lalacewar bututun hako danyen man fetur na Nigeria barazana ne ga tattara kudin shiga—CBN

0
51

Babban bankin Nigeria CBN, ya bayyana damuwar sa akan yadda bututun man fetur da ake amfani da shi wajen hako danyen man ya tsufa da kuma rashin yin aiki yadda ya kamata da cewa ya kawo koma bayan shirin da aka yi na hako ganganr danyen mai miliyan 2 kowacce rana a shekarar 2024.

Cikin wani rahoton tattalin arziki da CBN ya fitar yace an samu raguwar kudin shiga da ake samu a fannin mai da kaso 24.72.

Bankin yace adadin kudaden shigar yana samun koma baya a kowanne rubu’i sakamakon matsalolin da bututun man ke haifarwa.

Haka zalika CBN yace da wuya a iya cimma burin hako ganganr danyen mai miliyan 2 kowacce rana a wannan shekarar da take kokarin karewa, in har ba’a dauki matakan dakile matsalar lalacewar bututun man ba, da sauran kalubalen da ake fuskanta wajen hako man.

A wani cigaban bankin CBN yace an samu karuwar yawan man da ake hakowa daga ganga miliyan 1.27, zuwa 1.33, amma ayyukan masu satar danyen man da fasa bututun mai yana ragewa Nigeria yawan kudin shiga daga bangaren Mai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here