Soja ya kashe Matukin babur mai kafa uku ta hanyar caka masa wuka

0
56

Wani jami’in sojan dake aiki tare a barikin Rukuba, dake Jos, yayi sanadiyyar mutuwar wani Matukin babur mai kafa uku Mai Abdullahi Muhammad, ta hanyar caccaka masa wuka.

Jaridar Daily trust, ta rawaito cewa Matukin babur din ya kasance makiyayi.

Shugaban kungiyar cigaban Fulani, ta GAFDAN, Garba Abdullahi, ya sanar da manema labarai cewa sojan ya kashe matashin mai kimanin shekara 26, a kusa da kofar shiga barikin Rukuba a Jos, dake Plateau, inda yayi ala wadai da kisan tare da neman mahukuntan barikin su dauki matakin yiwa mamacin adalci.

Mai magana da yawun sashin da sojan ke aiki Laftanar Kanar Aliyu Danja, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shugaban kungiyar ta GAFDAN, yace lamarin ya afku, a lokacin da mamacin ya fita siyo wani abu, bayan ya dawo cikin babur din sa ya buge sojan ba tare da ya kula ba, wanda bayan haka ya fito tare da bawa sojan hakuri, ana tsaka da yin haka sojan ya kwadawa mai babur din Mari, da kuma dauko wuka ya rika caka masa a kirji.

Bayan caka wukar ne aka shiga da matashin asibitin barikin Rukuba, inda aka tabbatar da cewa ya rasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here