Kamfanonin sadarwa na Nigeria, MTN, Airtel, Glo da 9mobile, na shirin kara kudin kiran waya dana Data daga yanzu zuwa sabuwar shekarar 2025.
Wani jami’in fannin sadarwa, yace akwai tabbacin cewa kamfanonin sadarwa zasu samu sahalewar hukumar NCC don su kara kudin kiran wayar.
Jami’in da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana cewa kamfanonin sadarwar na MTN da Airtel da 9Mobile sun aike wa hukumar sadarwa ta kasa NCC buƙatarsu kuma alamu suna nuna cewa zasu yi nasara.
Kamfanonin sadarwar sun jima suna neman hukumar sadarwa ta kasa ta basu damar kara kudin kiran, fiye da shekara 10 data wuce.
Hukumar NCC ta ƙi amince wa kamfanonin ƙara kuɗi tun a zamanin tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami.