Dan ta’adda ya tashi Bom a gidan mutuwa a jihar Borno

0
72

Wani mai kunar bakin wake ya tashi Bom, lokacin da yaje yin gaisuwar mutuwa a yankin Dalori, dake jihar Borno.

Zuwa yanzu an bayar da rahoton cewa harin yayi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da jikkata mutum guda sakamakon harin.

Wata Majiyar tsaro tace dan kunar bakin waken daya tashi Bom, din ya samu damar yin hakan a lokacin da yayi kamar yazo yin gaisuwar mutuwa.

Jami’an tsaron da suka halarci wajen zaman makokin bayan tashin Bom din sun ce kawo yanzu an fara gudanar da bincike don gano musababbin kai harin kunar bakin waken.

An tsaurara matakan tsaro a yankin da akayi rasuwar dake Dalori, wanda tuni aka garzaya da wanda ya jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here