Gidajen man NNPC na Abuja sun fara sun fara siyar da litar fetur akan naira 965

0
55

Farashin litar man fetur ta sauka zuwa naira 965 a birnin tarayya Abuja.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa kamfanin mai na NNPC ya juya farashin sa a daukacin gidajen man dake birnin Abuja daga tsohon farashin Naira 1,060 zuwa naira 965.

Jaridar tace a babban gidan man NNPC dake Abuja dake akan titin Obasanjo, da Wuse zone 4, da Central Area, an canja farashin zuwa naira 965.

Rahotanni sun bayyana cewa tuni wadannan gidajen mai suka cika makil da masu ababen hawa don kwadayin samun saukin, sakamakon cewa mafi yawancin gidajen mai basu rage nasu farashin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here