CBN yace tattalin arzikin Nigeria ya inganta da kaso 3.46

0
72

Babban bankin kasa CBN ya sanar da cewa tattalin arzikin kasa ya inganta da kaso 3.46 zuwa rubu’i na uku cikin wannan shekara ta 2024, wanda a baya yake akan kaso 3.19.

:::Yan Nigeria 213 ne suka mutu sanadiyyar turmutsutsu a cikin shekaru 11

Bankin yace an samu wannan nasara daga wasu bangarorin samun kudin shiga da bana man fetur ba musamman kasuwanci.

Rahoton da CBN ya fitar ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ya ragu idan aka kwatanta da baya, sannan a cewar bankin an samu habbakar fannin kasuwanci.

A wannan yanayi da mafi yawa daga cikin al’umma ke cewa an samu koma bayan tattalin arziki, su kuwa hukumomin gwamnati musamman hasu hada-hadar kude cewa suke yi akwai ingantuwa a harkokin tattalin arziki.

Tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan masarufi na daga cikin babbar matsalar dake damun al’ummar Nigeria, da suke fatan samun sauki in har da gaske ana samun cigaba a fannin tatattalin arzikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here