Mutane 10 sun mutu a turmutsutsun karɓar tallafin Abinci a Abuja

0
35

Akalla mutane 10 ne aka bayar da labarin rasuwar su a safiyar yau asabar bayan wani turmutsutsu ya rutsa dasu a wata majami’a a unguwar Maitama dake birnin tarayya Abuja

Idan za’a iya tunawa a yan kwanakin nan an samu makamancin Wannan lamari a birnin Ibadan na jihar Oyo, da turmutsutsu yayi sanadiyyar mutuwar kananun yara 35 Sannan 6, suka ji munanan raunuka, wanda shima aka yi saboda neman tallafi.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa mutanen na yau sun mutu lokacin da suke kokarin karbar tallafin kayan abinci a majami’ar dake Maitama.

An shirya rabon kayan abincin da manufar tallafawa masu fama da kuncin rayuwa musamman masu rayuwa a kauyukan Mpape, Gishiri da sauran su.

Wani da abin ya faru a gaban idon sa yace mutanen sun rasu da misalin karfe 7 zuwa 8 na safiyar yau, lokacin da suke kokarin karbar tallafin kayan abinci.

Zuwa yanzu ba’a samu damar jin ta bakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Abuja kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here