Sojoji sun kashe jagoran yan ta’adda mai alaka Bello Turji a Sokoto

0
70
Sojoji
Sojoji

Dakarun Sojin Nigeria sun samu nasarar kashe rikakken dan fashin daji mai suna Bako Wurgi, biyo bayan musayar wutar da akayi tsakanin sa da jami’an tsaron a Sokoto.

Wurgi, ya kasance wanda ake nema ido rufe, sakamakon zargin cewa yana da hannu wajen kisan wani masarauci a Sokoto, tare da hada kai da dan ta’adda Bello Turji.

Daraktan yada labarai, na rundunar sojin Edward Buba, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa daya fitar.

Buba, yace sun samu bayanan sirri daga wajen jagoran yan ta’addan kafin mutuwar sa, wanda zasu taimaka a samu nasarar yakar ayyukan ta’addanci.

Rundunar sojin ta nemi al’umma su zama masu kiyayewa a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara, saboda yan ta’adda na yin amfani da lokutan wajen kai hare hare, inda rundunar tace tana kokarin dakile duk wata barazanar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here