Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya diyyar biliyan 8.5 ga wadanda ta rushewa Gini

0
70
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Wata babbar kotun Kano, ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Kano zata biya diyyar naira N8,511,000,000 , ga mamallakan ginin Lamash, wanda gwamna Abba Kabir Yusuf, ya rushe a baya.

Bayan haka a larabar data gabata kotun ta umarci masu kare kansu a karar da aka shigar mata wato Gwamnan Kano da Kwamishinan Shari’a na jihar dasu biya kamfanin Lamash Naira miliyan 10, a matsayin kudin da kamfanin ya kashe a harkokin shari’ar neman hakkin rushe masa ginin da akayi.

:::Tinubu ba zai cika alkawarin dake cikin kasafin shekarar 2025 ba—PDP

Idan za’a iya tunawa a watan Yunin shekarar 2023, gwamnatin Kano ta Rushe katafaten ginin Lamash, da ake yada jita jitar cewa mallakin iyalan tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, ne da gwamnatin tace an mallake shi ba bisa ka’ida ba.

Tun da farko masu wajen da aka rushe sun bayyanawa mai shari’a Sunusi Ma’aji, cewa sun mallaki wajen bisa tanadin doka a lokacin mulkin Ganduje.

Lauyan dake kare Lamash, a shari’ar Nureini Jimoh, shine ya gabatarwa da kotu kwafin shaidar takardun da suka mallaki wajen.

Ko a baya wata kotu ta umarci gwamnatin Kano, ta biya diyyar naira biliyan 30, ga mutanen da aka rushewa shaguna a filin idi, dake kwaryar Kano, sai dai har yanzu ba’a ji labarin biyan diyyar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here