An sace yan Nigeria fiye da miliyan 2 a cikin shekara guda

0
80

Wani binciken da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar ya nuna cewa an kashe yan Nigeria 614,937, tare da sace mutum miliyan 2 da dubu dari 2 cikin watanni 12, na shekarar 2023, zuwa 2024.

An fuskanci wannan kalubalen a tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilu na 2024.

An samu wannan alkaluma cikin rahoton NBS, da aka yiwa lakabi da binciken laifuka da tsaron al’umma a shekarar 2024.

Rahoton, yace masu garkuwa da mutane sun karɓi jimillar kuɗi Naira tiriliyan 2.2 a matsayin kuɗin fansa.

A cikin mutanen da aka sace miliyan 1.6 sun fito ne daga ƙauyuka, yayin da Yankin Arewa Maso Yamma ya fi yawan mutanen da aka sace na miliyan 1.4.

Rahoton, ya kuma nuna yawan kashe kashen da aka yi, inda yankin arewa maso yamma ke kan gaba da mutum 206,030, sai arewa maso gabas da mutum 188,992.

Yankin Kudu maso yamma shi ne yankin da ba a yi kashe-kashe da yawa ba, inda yake da mutum 15,693 kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here