Jami’an tsaron Nigeria sun kashe yan ta’adda dubu 8 a shekarar 2024

0
70

Jami’an tsaron Nigeria sun samu nasarar kashe yan ta’adda da yawan su yakai 8,034, daga farkon 2024 zuwa yanzu da ake yin bankawa da shekarar.

Ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ya bayyana hakan, sannan yace an kama wasu mutane 11,623 da ake zargi da ayyukan ta’addanci a cikin shekarar.

Bayan haka ance jami’an tsaron sun yi nasarar ceto mutane 7,967 da aka yi garkuwa da su, a cewar shugaban sashin shari’a na ofishin, Zakari Mijinyawa.

Mijinyawa yace an kwato makamai 10,200 da harsasai 224,709, daga hannun ’yan ta’adda a shekarar.

Ya ce jimillar mutane 30,313 aka kama a shekarar bisa zargin manyan laifuka, inda aka kwato motocin sata 1,438.

Jami’an tsaro sun kuma dakile satar danyen mai da yace kudinsa ya kai Naira biliyan 57.

Ya ce wannan nasarar ta samu ne a da hadin kan jami’an tsaro da amfani da kayan aiki na zamani da wajen aikinsu n a dakile ayyukan ba daidai ba a yankin Neja Delta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here