Kwankwaso ya ziyarci Olusegun Obasanjo

0
50

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, tare da ganawa da shi a gidan sa dake Abeokuta.

Kwankwaso tsohon É—an takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, a zaben shekarar 2023 ya ziyarci Obasanjon tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke.

Cikin wani saÆ™o da Rabi’u Musa Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar sun tattauna abubuwan da suka shafi Æ™asa, ciki har da makomar siyasar Nigeria.

A cewar Sanata Kwankwaso, Obasanjo, ya nuna musu karamci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here